Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiAn gabatarwar Majalisar wakilai kudirin kırkıro sabuwar jihar Eititi a yankın Kudu.

An gabatarwar Majalisar wakilai kudirin kırkıro sabuwar jihar Eititi a yankın Kudu.

Date:

Majalisar wakilai ta gabatar da ƙudurin ƙirƙiro ƙarin jiha guda da za a kira jihar Etiti a yankin kudu.

Ƙudirin wanda Amobi Godwin Omaha tare da wasu ‘yan majalisa huɗu suka gabatar – ya tsallake karatu na farko a majalisar jiya Talata.

Ƙudurin na buƙatar yin gyara a sashe na uku na kundin tsarin mulkin ƙasar nan domin goge lamba 36 tare da maye gurbinta da lamba 37 don bai wa sabuwar jihar damar shiga jerin jihohin ƙasar nan sannan a saka Etiti bayan Enugu cikin jerin sunayen jihohin ƙasar.

Sabuwar jihar da za a yanka daga duka jihohin yankin biyar za ta ƙunshi ƙananan hukumomi 11, inda Lokpanta da a yanzu ke cikin jihar Abia, zai kasance babban birninta.

Ƙananan hukumomin da za su koma sabuwar jihar sun haɗa da Isuikwuato da Umu-Nneochi (jihar Abia), da Orumba ta Arewa da Orumba ta kudu (jihar Anambra), sannan Ivo da Ohaozara (jihar Ebonyi), sai Aninri da Agwu da Oji River (jihar Enugu), da kuma Okigwe da Onuimo (jihar Imo).

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...