Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiAkwai daure kai cikin hukuncin da alkalin babbar kotun tarayya dake nan...

Akwai daure kai cikin hukuncin da alkalin babbar kotun tarayya dake nan Kano AM Liman yayi kan dambarwar masarautar Kano.

Date:

Wani farfesa a fannin shari’a yace akwai daure kai cikin hukuncin da alkalin babbar kotun tarayya dake nan Kano AM Liman yayi kan dambarwar masarautar Kano.

A wata zantawartsa da jaridar dailytrust masanin Shari’a Farfesa Auwalu Yadudu yace hukuncin na cike da rudani da kwan gaba kwan baya.

Yadudu yace irin wannan hukunci baya taimakawa cigaban lamurran shari’a, musamman yadda alkalin yace yana da hurumin sauraron karar kan hakkin dan’adam na mai kara da aka take wajen tsigeshi ba bisa ka’ida ba, amma a gefe guda alkalin yace bashi da hurumin rushe dokar da gwamnatin Knao tayi wadda ta rushe masarautun jihar 5 da kuma nade naden da suka biyo bayan ta ciki har da nadin sarkin dawaki babba, wanda wannan abin daure kai ne matuka.

Farfesa Yadudu yace baya zargin alkalin da aikata ba dai dai ba, amma dai ta yaya za a ce an jingine abubuwan da doka ta zo dasu, ba tare da tantance halaccin dokar ba.

 

 

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...