Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiƘungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Date:

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar Hamas ta isa birnin Al’Qahira, yayin da aka sake farfado da zaman tattaunawa domin tsagaita wuta a hare-haren da sojojin Isra’ila ke kaiwa Falasdinawa a yankin Gaza.

An tabbbatar da cewa, jami’an Hamas uku da suka taso daga birnin Doha a kasar Qatar, sun sauka a jirgin sama domin tattaunawa da sauran wakilai masu ruwa-da-tsaki dangane da yadda za’a yi musayar Falasdinawa fursunoni da ke gidajen Yarin Isra’ila, da Yahudawan da aka yi garkuwa dasu ranar 7 ga watyan Oktobar bara.

Wata kafar labaran Isra’ila ta ce Shirin da ke hannu shi ne na musayar mutane 33 da Hamas ke garkuwa dasu, da daruruwan fursunonin Falasdinawa, da suka hada da tsofaffi, da sojoji mata, da masu tabin hankali.

Karkashin wannan yarjejeniya, tilas ne kuma Isra’ila ta janye sojojinta daga kan wata babbar hanya da ta raba zirin Gaza gida biyu.

Yanzun haka dai mafi rinjayen mazauna wannan yanki sun tsere zuwa kudancin Gaza daga arewa domin tsira da rayukansu.

Sai dai kuma tana-kasa-tana-dabo, domin masu sharhi na ganin tilas Firaminista Benjamin Netanyahu ya zabi abu daya, tsakanin musayar wadanda Hamas ke rike dasu, da dorewar gwamnatinsa.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...