Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaƘungiyar ƴan jarida ta kasa ta umarci mambobinta da su shiga yajin...

Ƙungiyar ƴan jarida ta kasa ta umarci mambobinta da su shiga yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago ta ƙasar NLC da TUC suka shiga.

Date:

Ƙungiyar ƴan jarida ta kasa ta umarci mambobinta da su shiga yajin aikin da manyan ƙungiyoyin ƙwadago ta ƙasar NLC da TUC suka shiga a kan dambarwar mafi ƙanƙantar albashi a ƙasar.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun Babban Sakatarenta, Achike Chude, a jiya Lahadi, ƙungiyar ta umarci dukkanin shugabanninta a matakai daban-daban a jihohin ƙasar har da Abuja su tabbatar ƙungiyar ta shiga yajin aikin, domin mara baya ga manyan ƙungiyoyin ƙwadagon.

Rahotanni na nuna cewa yajin aikin na gama-gari da manyan ƙungiyoyin ƙwadagon suka shiga daga yau Litinin na samun karɓuwa a fadin ƙasar, yayin da shugabannin ƙwadago ke bi ma’aikatu da sauran wuraren aiki a jihohi har ma da Abuja babban birnin ƙasar domin tabbatar da ma’aikata sun ƙaurace wa wuraren aikin.

 

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...